‘Yansanda Sun Kuɓutar Da Matashin Da Ake Zargi Da Yaga Alƙur’ani A Kano


Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta ceto wani matashi da ake zargi da yaga Alƙur’ani daga fusatattun matasa a wani otel a yankin Badawa na birnin Kano.

Ƙwararren mai sharhi kan masu tada ƙayar baya, Zagazola Makama, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:45 na dare a ranar Asabar, 21 ga Disamba, a Otel din Sarina da ke Badawa.

  • AFCON 2025: Ƙasashe 5 Da Za Su Iya Lashe Gasar Nahiyar Afirka
  • Bukukuwan Kirismati Da Sabuwar Shekara: ‘Yansanda Sun Ƙara Tsaurara Tsaro A Kano

Makama, da yake bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Litinin, ya ce majiyoyi sun bayyana cewa, wasu matasa uku da ake kira Musa Tasiu, Awwal Ibrahim da Soja Snu, dukkansu mazauna unguwar Dorayi, sun shiga otel din, inda aka yi zargin cewa daya daga cikinsu, Musa Tasiu, ya shiga masallacin otel din, ya lalata kofar sannan ya ɗauki Alqur’ani mai tsarki ya yaga shi.

Bayan zargin, an ruwaito cewa mutanen da ke cikin harabar otel din sun taru da yawa suna shirin kai wa wanda ake zargin hari.

Cikin gaggawa, tawagar jami’an tsaro da ke aiki a yankin ta amsa kira, inda ta kuɓutar da wanda ake zargin sannu suka kwantar da tarzomar da ke shirin tasowa.

Yayin da yake tabbatar da lamarin ga wakilinmu, kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin yana hannun ‘yansanda.

“Yanzu haka yana tare da mu kuma za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike,” in ji Kiyawa.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *