Xi Ya Taya Jose Antonio Kast Murnar Lashe Zaben Shugaban Chile
[ad_1]
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna a yau Litinin ga Jose Antonio Kast kan zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar Chile.
Xi ya yi nuni da cewa, kasar Chile ta kasance kasa ta farko ta kudancin Amurka da ta kulla huldar diflomasiyya da jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kuma kasashen biyu a koyaushe suna tsayawa tsayin daka wajen mutunta juna, da daidaito, da samun moriyar juna, da hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare.
Xi ya ce, yana dora fifiko sosai kan bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Chile, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da zababben shugaban kasar Kast, don ci gaba da sada dadadden zumuncinsu, da daukaka dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Chile zuwa wani sabon matsayi na koli, da samar da karin moriya ga jama’ar kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link