’Yan bindiga sun kashe mutum 4 sun sace 10 a Zamfara
[ad_1]
’Yan bindiga sun kashe mutane hudu tare da yin garkuwa da aƙalla mutane goma ciki har da yara a garin Maru, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Maru da ke Jihar Zamfara, a daren jiya Lahadi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Maru, Honorabul Bello Jabaka, ya ce “Eh, gaskiya ne ’yan bindiga sun kai hari a garin Maru, kuma a halin da nake magana da ku yanzu muna shirye-shiryen jana’izar mutanen huɗu da aka kashe. Ku bari mu kammala kafin in ba ku cikakken bayani.”
Wani ganau, Malam Ibrahim Hamida, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun shigo garin ne ta gefen kogin da ke gabashin Maru, kuma sun shafe sama da sa’a guda suna gudanar da ta’addancin kafin su watse.
“Sun shigo garin ne da misalin karfe 12 na dare, kuma harin ya ci gaba har zuwa ƙarfe 1:30 na safe.
“Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, ya jikkata wasu, sannan aka yi garkuwa da aƙalla mutane goma ciki har da yara. Waɗanda suka jikkata suna karɓar magani a asibiti.”
Ibrahim ya ƙara da cewa, “Har yanzu ba mu tantance adadin waɗanda aka yi garkuwa da su ba, amma tabbas sun ɗauki akalla mutane goma ciki har da yara. Sun kashe mutane hudu ciki har da matar wani ɗan sanda, sannan sun yi garkuwa da ’ya’yansa ma.”
Al’umma sun yi fito-na-fito da ’yan ta’adda
Malam Ibrahim ya ƙara da cewa, al’ummar garin sun fito da ƙarfin hali suka fuskanci ’yan bindigar bayan an kira salla a masallatai a matsayin alamar kiran jama’a da su fito da makamai domin kare kansu.
“Sojoji sun yi gaggawar mayar da martani, kuma jama’a sun taka muhimmiyar rawa wajen tarwatsa ’yan bindigar.
“An kira salla a masallatai domin sanar da jama’a su fito da makamai su kare kansu, kuma jama’a sun amsa kiran.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link