Kungiyar Wasan Ƙwallon Dawakin Katsina ta zaɓi sabbin shugabanni




A ranar Asabar, 20 ga watan Disamba, 2025, Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Dawaki (Polo) ta gudanar da zaben sabbin shugabanninta a Katsina.

Zaben ya biyo bayan buƙatar da ’ya’yan ƙungiyar suka gabatar na a zaɓi shugabanni masu wa’adi daga hannun masu riƙon ƙwarya.

An gudanar da zaben shugabanni 13 waɗanda suka nuna sha’awar neman jagorancin ƙungiyar.

An zabi shugabanni 9 ba tare da hamayya ba, yayin da sauran mukamai 4 — Babban Sakatari, Mataimakin Sakatari, Jami’in Hulɗa da Jama’a, da kuma Mataimakin Kyaftin, su ne suka shiga cikin takarar da ta samu hamayya.

Kujerun da ba a yi hamayya a kansu ba sun haɗa da kujerar Shugaba da mataimakansa biyu, Ma’aji, Sakataren Kuɗi, Mai Bincike, Kyaftin, Shugaban Kula da Filin da Wuraren Ajiye Dawaki, da Mai Bayar da Shawara ta Fuskar Shari’a.

Alhaji Muhammadu Usman Sarki shi ne zaɓaɓɓen Shugaba tare da Dokta Aminu Waziri da Lawal Mangal a matsayin mataimaka.

Kujerar Babban Sakatari ta faɗa hannun Alhaji Ibrahim Daku, shi kuwa Kyaftin na ƙungiyar, Alhaji Ibrahim Usman Sarki, ya sake zama zaɓaɓɓe.

Sani Lawal ya lashe kujerar Ma’aji, Alhaji Danbaba Yusuf shi ne Sakataren Kuɗi, sai Hamza Sule Maiyawo a matsayin Mai Bincike.

Barista Abdu Ladan Ƙofar Soro ya zama Mai Bayar da Shawara ta fuskar Shari’a,  Kujerar Mataimakin Sakatare ta shiga hannun Abubakar Abdulaziz, yayin da Amadu Balaho ya lashe kujerar Mataimakin Kyaftin.

Shugaban Fili da Wajen Ajiye Dawaki, Abba Kangiwa, ya ci zaɓen wannan kujera. Alhaji Nasiru Muhammad Wali ya zama Jami’in Hulɗa da Jama’a.

Sabon shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammadu Usman Sarki, a jawabinsa, ya yi fatan Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da aka ɗora a kansu.

Haka kuma, ya miƙa godiya a madadin zaɓaɓɓun shugabannin da suka yi nasara, tare da neman haɗin kan kowa domin ci gaban ƙungiyar.

Ya jaddada cewa waɗanda aka zaɓa su sani cewa ba don su zauna ba ne, sai don kawo ci gaban ƙungiyar, domin sake maido da wannan matarba ta Katsina a matsayin gidan wasan Polo.

Shi kuwa Mataimakin Shugaban ƙungiyar na dindindin, Karshin Katsina, Alhaji Sanusi Kabir, ya bayyana cewa an kafa tarihi tun shekaru 100 da suka wuce, wanda ba a taɓa yin zaɓe irin wannan ba.

Ya kuma jinjina wa kwamitin da ya shirya kuma ya gudanar da wannan zabe cikin nasara.

Barista Zahraddeen Sani daga Babbar Kotun Majistare ta Biyu da ke Katsina ya rantsar da zababbun shugabannin bisa jagorancin Shugaban Kwamitin Zaɓe, Alhaji Abdulwahab Sani Sito.

An gudanar da zaben lafiya ba tare da wata hayaniya ko rashin gamsuwa daga masu takarar mukaman da aka yi hamayya ba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *