Sarakuna sun goyi bayan Gwamnatin Gombe kan yaƙi da cin zarafin mata
[ad_1]
Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Gombe ƙarƙashin Kwamishina, Asma’u Muhammad Iganus, ta ziyarci masarautun Nafada da Funakaye domin ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da cin zarafi ga mata da yara.
A ziyarar ta farko a Masarautar Nafada, Kwamishiniyar ta ce alƙaluma sun nuna cewa cin zarafi ya kai kashi 87.46 a jihar.
Ta ce ya ce ya zama dole a haɗa kai da sarakunan gargajiya don kawar da matsalar.
Sarkin Nafada, Alhaji Muhammad Dadum Hamza, ya yi tir da yawaitar laifukan aikata fyaɗe a yankin.
Ya bayyana cewa babu wani gurbi da mai laifin aikata fyaɗe zai samu mafaka.
Ya ce za su tabbatar da an hukunta duk wanda aka kama, tare da goyon bayan ƙarin hukuncin ɗaurin sama da shekaru 14 da doka ke yi a yanzu.
A Masarautar Funakaye, Sarkin Funakaye, Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga IV, ya nuna cikakken goyon bayansa ga matakin gwamnati.
Ya ce ba za a yi wa masu aikata fyaɗe sassauci ba, domin hukunci mai tsanani shi ne zai rage aikata laifin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Funakaye, Alhaji Abdurrahman Shua’ibu Adam, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki tare da ma’aikatar domin kare mata da yara.
Kwamishiniyar, ta miƙa kundin Dokar VAPP ga masarautar Funakaye domin fara aiki da shi kai-tsaye.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link