Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Ga Japan Da Ta Zurfafa Tunani Tare Da Gaggauta Gyara Kura-kuranta
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga Japan da ta zurfafa tunani, tare da gaggauta gyara kura-kuran da ta tafka, maimakon ci gaba da dagewa wajen bin gurguwar hanya.
Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi tsokacin ne yayin wata zantawa da manema labarai bayan kammala ziyarar aiki a kasar Kyrgyzstan, da Uzbekistan da Tajikistan, inda ya yi tattaunawa mai ma’ana tare da takwarorinsa na kasashen uku, tsakanin ranakun 19 zuwa 22 ga watan Nuwamban nan.
Ministan ya ce idan har Japan ta ci gaba da nacewa wannan hanya, tare da aikata irin wadannan kura-kurai, dukkanin kasashe, da al’ummun dake goyon bayan adalci, na da ikon sake nazarin laifukan da kasar ta tafka a tarihi, suna kuma da nauyin aiwatar da matakan dakile sake komawar Japan amfani da karfin soji.
Wang, ya ce abu ne mai tayar da hankali, ganin yadda shugabar Japan mai ci ta fito fili, tana aikewa da mummunan sako, mai kunshe da yunkurin amfani da karfin soji dangane da batun yankin Taiwan. A cewarsa, hakan abu ne da bai dace a ji shi ba, kuma tsallaka jan layi ne da ba za a lamunta ba.
Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar Sin, na mayar da martani mai karfi, ba kawai domin kare ikon mulkin kai da tsaron yankuna ba, har ma da kare nasarorin da aka cimma, bayan tsallake tarin wahalhalu, zubar da jini da sadaukarwa yayin yakin duniya na biyu, tare da goyon bayan tsarin adalci na kasa da kasa da mutumtaka. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link