Kasashe Nawa Ne Suka Samu Tikitin Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?



Kawo yanzu dai mafarkin Nijeriya ya kare game da batun zuwa gasar kofin duniya ta 2026 bayan ta sha kashi a hannun Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a ranar Lahadi. Hakan na nufin cewa Nijeriya ba za ta halarci gasar ba karo na biyu a jere.

Kasashen Scotland da Belgium da Croatia sun kasance kasashen da a baya-bayan nan daga nahiyar Turai da suka samu gurbi a Gasar ta Kofin Duniya ta 2026 da za a yi a kasashen Amurka da Medico da kuma Canada.

Kawo yanzu kasashe 42 sun samu gurbi, da suka hada da Ingila da Faransa da Portugal da Norway da Jamus da Crotia da Netherlands Argentina mai rike da kofin da Cape Berde bakin gasar da Jordan da kuma Uzbekistan.

Masu Masaukin Baki: Kanada, Mexico, Amurka.

Yankin Asia: Australia, Iran, Japan, Jordan, Katar, Saudi Arabia, South Korea, Uzbekistan Nahiyar Afirka: Algeria, Cape Berde, Egypt, Ghana, Ibory Coast, Morocco, Senegal, South Africa, Tunisia.

Concacaf: Curaçao, Haiti, Panama.

Nahiyar Turai: Austria, Belgium, Croatia, Ingila, Faransa, Jamus, Portugal, Scotland, Switzerland.

Yankin Oceania: New Zealand

Kudancin Amurka: Argentina, Brazil, Kolumbia, Ekucador, Paraguay, Uruguay.

Ya zuwa yanzu akwai gurabe 18 da suka rage a gasar, da yawa daga cikinsu kuma daga nahiyar Turai ne.

Australia da Iran da Japan da Jordan da Katar da Saudiyya da Koriya ta Kudu duka sun samu gurabe daga yankin Asiya. New Zealand ta samu gurbi guda daya da aka ware wa yankin Oceania.

Daga nahiyar Afirka kuwa, Tunisiya da Morocco ne suka fara samun gurbi a gasar, daga baya kuma kasashen Aljeriya da Cape Berde da Masar da Ghana da Ibory Coast da Senegal da kuma Afirka ta Kudu – wadda za ta buga gasar karon farko tun 2010 da ta karbi bakuncin gasar.

A yankin Kudancin Amurka kuwa kasashen Brazil da Ecuador da Uruguay da Paraguay kuma Colombia na daga cikin kasashen yankin da suka samu gurbi ya zuwa yanzu.

Duk da cewa kasashen, Bolibia da New Caledonia ba su samu gurbi kai-tsaye ba, amma za su buga wasannin neman gurbi na nahiyoyi a watan Maris na 2026.

Kasashen da suka samu gurbin Gasar Kofin Duniya ta 2026

Masu Masaukin Baki: Canada, Medico, United States

Yankin Asia: Australia, Iran, Japan, Jordan, Katar, Saudi Arabia, South Korea, Uzbekistan

Nahiyar Afirka: Algeria, Cape Berde, Egypt, Ghana, Ibory Coast, Morocco, Senegal, South Africa, Tunisia

ConcaCaf: Curacao, Haiti, Panama

Nahiyar Turai: Austria, Belgium, Croatia, Ingila, Faransa, Jamus, Portugal, Switzerland.

Yankin Oceania: New Zealand

Kudancin Amurka: Argentina, Brazil, Colombia, Ecuador, Paraguay, Uruguay

Ya tsarin wasannin neman gurbin yake?

Kowace daya daga cikin hukumar kwallon kafa ta FIFA ta nahiyoyi na amfani da hanya ta daban domin tantance kasar da za ta samu gurbin Gasar Kofin Duniyar da ake yi duk bayan shekara hudu.

Oceania ne yanki daya da ya kammala nasa wasan neman gurbin, wanda dama gurbi daya aka tanadar masa.

Daga cikin tawagogi 48 da za su halarci gasar, tuni aka ware wa kasashe ukun da za su karbi bakuncin gasar gurabe, sai kuma gurabe 43 da sauran kasashen duniya za su samu ta hanyar samun gurbi kai-tsaye, daga nahiyoyin duniya shida.

Sai kuma ragowar gurabe biyu da za a samu ta hanyar buga wasannin cike gurbi tsakanin nahiyoyin.

Nahiyar Turai

Guraben da aka ware wa nahiyar: 16

Kasashen da suka samu gurbi kawo yanzu: Croatia, England da France da Portugal da Netherland da Sifaniya da Belgium da Jamus da Norway.

An raba kasashen nahiyar zuwa rukuni 12, wadanda suka kare a mataki na daya a kowane rukuni za su samu gurbi kai-tsaye don zuwa gasar. Su kuma kasashe 12 da suka kare a mataki na biyu a rukunonin, za su buga wasannin cike gurbi, tare da kasashe hudu da suka fi yawan maki a matakin rukuni na gasar UEFA Nations League da ba su samu gurbin zuwa Kofin Duniyar ba.

A cikinsu ne za a tantance kasashe hudu da za su samu karin guraben nahiyar Turai a Gasar Kofin Duniyar. Turai ce kawai nahiyar ba ta da wakilci a gasar cike gurbi ta nahiyoyi.

Kudancin Amurka

Guraben da aka ware wa nahiyar: Shida, da kasa daya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi

Kasashen da suka samu gurbi: Argentina, Brazil, Colombia, Ecuador, Paraguay da kuma Uruguay.

Wadda za ta je gasar cike gurbi ta nahiyoyi: Bolibia, Yankin Asia.

Guraben da aka ware wa nahiyar: Takwas, da kasa daya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.

Kasashen da suka samu gurbi: Australia, Iran, Japan, Jordan, Katar, Saudi Arabia, South Korea da Uzbekistan Kasashen UAE da Iraki za su kara tsakaninsu don tantance wadda za ta je gasar cike gurbi ta nahiyoyi.

Nahiyar Afirka

Guraben da aka ware wa nahiyar: Tara, da kasa daya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.

Kasashen da suka samu gurbi: Algeria, Cape Berde, Egypt, Ghana, Ibory Coast, Morocco, Senegal, Afirka ta Kudu da Tunisiya. Kasar da za ta je gasar cike gurbi ta nahiyoyi: DR Congo

Arewaci da tsakiyar Amurka da yankin Caribbean

Guraben da aka ware wa yankunan: Shida (ciki har da ukun da za su karbi bakunci), da kasashe biyu da za su buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.

Kasashen da suka samu gurbi: Canada, Medico da Amurka, wadanda suka samu kai-tsaye.

Yankin Oceania

Guraben da aka ware wa yankin: Daya, da kasa daya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.

Kasar da ta samu gurbi: New Zealand

Kasar New Caledonia, za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi – wadda ta kunshi kasashe daga Afirka da Asia da kudancin Amurka da Arewacin Amurka.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *