Ina tausaya wa mai mata ɗaya — Mijin Regina Daniels

[ad_1]



Ɗan Majalisar Dattawa na daga Jihar Delta, Sanata Ned Nwoko ya ce yana tausaya wa manza masu mata ɗaya, saboda a cewarsa, auren mace fiye da ɗaya yana sama wa maza daidiato da natsuwa.

Sanata Nwoko shi ne mijin shahararriyar jarumai Regina Daniels — kuma Kirista ne amma yake da mata huɗu, ya bayyana haka ne a yayin hirar da ka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.

“Ina tausaya wa mai mata ɗaya, ƙaddara a ce mutum ne ke tsaye da ƙafa ɗaya — ai akwai wahala. Amma kana da biyu ko uku ko huɗu za ka fi samun daidaito. Wannan shi ne ɗan misalin da zan ba ka,” in ji Sanata Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa.

Da gabatar da shirin ya tunatar da shi cewa a matsayinsa Kirista, Baibul ya haramta auren fiye da mace ɗaya, sai sanatan, ya kada baki ya ce, “Tsohon Alƙawari ya halasta auren fiye da mata ɗaya, ni mai bin addini ne, amma ba wannan muke tattaunawa ba a nan.”

Sanata Nwoko ya jaddada cewa ko kaɗan ba ya yin nadamar auren mata huɗu da yi.

“Ba ni da wani abin da-na-sani. Kuma zan ƙara. Ya kamata mutum ya auri wanda yake so ya aura” in ji shi.

Ya kuma yi watsi da zargin tashin hankali tsakaninsa da matarsa, fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Regina Daniels, a matsayin ƙarairayi.

“Ni ba mutum mai tashin hankali ba ne. Ina mutunta Matana kuma ina ƙaunar su da ’ya’yana,” in ji shi.

Bayanin nasa na zuwa ne bayan rahotannin da suka maye kafofin sada zumunta game da hatsaniya tsakaninsa da Regina Daniels ta wallafa wani katafaren gidan da ta ce ya gina mata,mita da sauran iyalansa.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *