Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi

[ad_1]



Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi.

A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

Abdulmumin Jibrin ya sanar ta shafinsa cewa sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa. “Na samu kyakkyawar tarba daga dubban al’ummar mazaɓata ta Kofa, Bebeji, da ke Jihar Kano.

“Taron ya yi ittifaƙin ficewa daga NNPP/Kwankwasiyya, mu koma APC, tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi wa’adi na biyu.

“Kafin nan, malamai kimanin 2,000 daga mazaɓarmu sun gudanar da addu’o’i na musamman ga Shugaban Ƙasa da neman samun zaman lafiya da ci-gaban Ƙiru/Bebeji, Kano, da ma Najeriya baki ɗaya.”

Idan ba a mata ba, Jam’iyyar NNPP ta dakatar da ɗan majalisar ne bisa zargin yi mata zagon ƙasa da kuma rashin kuɗin ƙa’ida na jam’iyya.

Tun bayan lokacin ba a ji daga gare shi ba game da makomar siyasarsa, duk da cewa makusantansa sun bayyana cewa yana ɗasawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC, wanda ya kawo hasashen yiwuwar komawarsa APC.

A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar ta shafinsa cewa ya sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa.

A ɗaya daga bidiyoyi daya wallafa, an ga ɗan majalisar yana jawabi ga magoya bayansa da cewa zai sauya sheƙa tare da magoya bayansa domin kauce wa kuskurensa na baya na sauya sheƙa shi kaɗai.

“Na yanke shawarar zuwa da wannan taron jama’a domin gyara kuskuren da na yi a baya. Kada daga baya wani ya zo yana cewa ai ba Ni da magoya baya.”

Daga nan ya tambaye su ko sun yarda su fice daga NNPP da Kwankwasiyya zuwa APC, inda suka yi ta shewa suna cewa “APC.”

Daga nan ya tambaye su wanda za su zaɓa a 2027, sai suka amsa cewa “Tinubu.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *