Rikicin shugabanci ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe

[ad_1]



Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, ta sanar da korar tsohon ɗan takarar gwamna na shekarar 2015, Nafiu Bala, bisa zargin cin amanarta.

Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Gombe.

A cewarsa, kwamitin ladabtarwa na unguwar Nasarawo ya binciki Bala, inda ya same shi da laifukan cin amanar jam’iyyar wanda hakan ya saɓa wa dokokinta.

Ya ce an gayyaci Bala domin ya kare kansa a gaban kwamitin amma ya ƙi bayyana.

Barde ya ƙara da cewa kwamitin zartarwa na jihar, ya tabbatar da wannan hukunci, kuma sun aike wa shugabancin jam’iyyar na ƙasa domin ɗaukar matakin na gaba.

Haka kuma ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar a jihar an tsige su daga muƙamansu.

Duk da ɗaukar wannan mataki, Nafiu Bala, ya yi watsi da shi, ya bayyana cewa shi ne halastaccen shugaban riƙo na ADC a jihar.

Ya ce an zaɓe shi ne bisa tsarin jam’iyyar da kuma taron gangamin da aka gudanar.

Bala, ya ƙara da cewa tun daga shekarar 2022 aka kori Auwal Abba Barde daga jam’iyyar, don haka ba shi da ikon ladabtar da shi ko ɗaukar wani mataki a kansa.

Ya yi nuni da cewa kundin tsarin mulkin ADC da dokokin Najeriya suna buƙatar duk wanda aka kora daga jam’iyyar ya sake yin rajista daga matakin unguwa kafin ya dawo cikinta.

A cewarsa, hakan ya sa ba ya ɗaukar hukuncin da aka ɗauka a kansa da muhimmanci.

Ya kuma bayyana cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta amince da shi a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

Bala ya jaddada cewa zai ci gaba da jagoranci domin tabbatar da gaskiya da haɗin kai a jam’iyyar, sannan ya gargaɗi waɗanda ke ƙoƙarin tada zaune-tsaye a ADC.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *