Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

[ad_1]


A yau Litinin ne kasar Sin ta musanta zargin da shugaban Amurka ya yi mata, cewa wai kasar tana yin gwajin makaman nukiliya a asirce, tana mai bayyana aniyarta ta amfani da tsarin nukiliya na tsaron kai, tare da cika alkawarin da ta dauka na dakatar da gwajin nukiliya.

Yayin taron manema labarai na yau din, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta shaidawa manema labarai cewa, a matsayinta na membar dindindin a kwamitin tsaron MDD, kuma mai kiyaye makaman nukiliya da ta mallaka, Sin tana aiwatar da manufar kin fara amfani da makaman nukiliya, da goyon bayan hurumin cikakkiyar yarjejeniyar hana gwajin nukiliya ko CTBT.

Mao, ta kuma bayyana fatan ganin Amurka ta martaba nata alkawuran, karkashin yarjejeniyar ta CTBT, kana ta wanzar da matakin dakatar da gwajin nukiliya, kuma ta aiwatar da kwararan matakai na mara baya ga yarjeniyoyin kwance damara da hana bazuwar makamai.

Kafin hakan, a jiya Lahadi, sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent, ya zargi kasar Sin da ci gaba da dakile fitar da ma’adanan farin karfe na “rare earth”, don haka a cewarsa mai yiwuwa Amurka ta kakabawa Sin takunkumai. Game da hakan, Mao Ning ta ce mahukuntan Sin sun sha bayyana matsayar kasar dangane da manufofi masu nasaba da tantance fitar da ma’adanan na “rare earth”.

Mao, ta ce sakamakon tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin Sin da na Amurka a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysiya, ya nuna yadda shawarwari, da hadin gwiwa suka zamo hanya mafi dacewa ta warware matsaloli, kuma barazana da matsin lamba ba za su bayar da wata gudummawa ta warware batutuwa ba.

Jami’ar ta kara da cewa, matakin gaggawa da ya dace Sin da Amurka su runguma, shi ne aiwatar da muhimmiyar matsaya da aka cimma, yayin ganawar shugabannin Sin da Amurka a Busan na kasar Koriya ta Kudu, da ingiza karin daidaito cikin harkokin raya tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayyar Sin da Amurka, da ma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *