Masu yabon Buhari sun yi masa ba’a bayan ya sauka daga mulki —Gwamna Sule

[ad_1]



Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce wasu daga cikin mutanen da saba yabon tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari lokacin yake kan mulki, su ne suka fara yi masa ba’a tare da suka bayan ya sauka daga mulki.

Da yake jawabi a wani taron “Lakcar Raymond Dokpesi” da Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) ta shirya a birnin Abuja, Gwamna Sule ya ce ya shaida da idonsa yadda wasu ’yan siyasa ke yabo da fadanci a gaban Buhari, amma daga bisani su sauya baki sheƙa da zarar shugabannin sun bar mulki.

Ya ce, “Tun da na zama gwamna, na ga abin da son kai da kwaɗayi ke iya haifarwa. Na ga mutane suna zaune a gaban Shugaba Buhari suna cewa, ‘Kai ka fi kowa, babu wanda zai iya yin wannan kamar kai.’

“Amma bayan saukar Buhari daga mulki, sai suka fara cewa, ‘Ai, yana cikin shugabannin mafiya rauni.’ Waɗannan mutanen ɗaya ne, amma lokaci ne ya bambanta. Wannan shi ne kwaɗayin yabo da son kai,” in ji shi.

A wajen taron, an karrama Gwamna Sule da kyauta da kuma lambar girmamawa ta NIPR, inda ya bayyana farin cikinsa da irin jarumtakar marigayi Cif Raymond Dokpesi, wanda ya kafa tashoshin rediyo da talabijin na farko masu zaman kansu a ƙasar tun lokacin mulkin soja.

“Ina nan ne don mu taya murna da tunawa da gwarzon kafafen yaɗa labarai. Dokpesi mutum ne mai gaskiya da jajircewa wajen faɗin gaskiya ga masu mulki, ko da a lokutan da suka fi wuya,” in ji Gwamna Sule.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *