’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa
[ad_1]
’Yan Sanda sun sake kama dan gwagwarmaya kuma mamallakin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, bayan wata kotun Majistare da ke Abuja, ta bayar da belinsa.
An sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa tare da wasu mutum 12 a ranar Juma’a.
Alƙalin kotun, Abubakar Sai’id ne, ya bayar da belin Sowore da wasu mutum 12 da aka tuhuma da tayar da hankalin jama’a, sakamakon zanga-zangar Yanar Gizo da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.
Lauyan Sowore, Tope Temokun, ya zargi ’yan sanda da yin amfani da karfi, inda suka yi awin gaba ba tare da wani bayani ba.
Temokun ya bayyana cewa: “Bayan kotu ta bayar da belin Sowore, sai wasu ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin CSP Iliyasu daga Sashen CID suka mamaye harabar kotun, inda suka sa masa da sauran jama’ar da ke wajen duka, sannan suka tafi da Sowore a bainar jama’a.
“A kokarin dakatar da su na ji rauni.”
Ya ƙara da cewa ba a kai Sowore gidan yari ba, amma an tafi da shi wani waje daban wanda ba wanda ya sani.
Kotun ta bayar da belin Sowore da sauran waɗanda ake tuhuma; ciki har da Aloy Ejimakor lauyan shugaban IPOB Nnamdi Kanu da kuma ɗan uwan Nnamdi Kanu, Emmanuel Kanu, kan kudi Naira 500,000 kowanne.
Kotu ta kuma umarce su da su miƙa fasfo ɗinsu, tare da katin shaida dan kasarsu da takardun biyan haraji na shekaru uku kafin a sake su.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ’yan sanda ba su fitar da wata sanarwa ba game da sake kama Sowore ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link