An zabi sabuwar firaminista a Luthuania

[ad_1]



Shugaban ƙasar Lithuania, Gitanas Nauseda, ya zabi ’yar majalisa Inga Ruginiene ta jam’iyyar Social Democrat, a matsayin firaminista, bayan Gintautas Paluckas ya yi murabus sakamakon binciken rashawa da ake gudanarwa a kansa.

Sai dai Ruginiene ta taba fuskantar suka kasancewar tana da alaka da ’yan uwa a Rasha, wadanda ta ziyarta a shekarun 2015 da 2018.

Sai dai ta ce yanzu daina kai musu ziyara, kuma ta jaddada cewa tun farko Ukraine take mara wa baya a yakin da take yi da Rasha, wadda ta kaiwa mamaya a 2022.

Majalisar dokokin ƙasar za ta amince da nadinta tare da ministocinta kafin ta kama aiki.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Paluckas ta yi murabus, bayan jam’iyyar Democrat  ta janye goyon bayan hadin gwiwar da ke kunshe da jam’iyyar populist ta Nemunas Dawn, lamarin da ya haifar da rikicin siyasa.

Hukumar kula da laifukan kudi (FNTT) ta kama ɗan uwan Paluckas a ranar Alhamis tare da wasu mutum huɗu a wani bincike kan kamfanonin da ake alaka da tsohon firaministan.

Sai dai har yanzu babu wata tuhuma da aka gabatar a kan Paluckas.

Tasha


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *