Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano




Mahukunta sun kai samame tare da rufe wani gidan shan Shisha da ke kan titin Abdullahi Bayero a cikin ƙwaryar birnin Jihar Kano.

Bayanai sun ce wata rundunar haɗin gwiwa ce ta kai samamen da ta ƙunshi jami’an ukumar Kula da Yawon Buɗe Ido da kuma na Hukumar Hana Sha da Fataucin Ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano, da Hukumar ’Yan Sanda a Jihar Kano.

Wannan na cikin wata sanarwa da Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano ta fitar a ranar Asabar, inda ta ce jami’an NDLEA sun kama wasu kayan maye da kuma wasu mutane da ake zargi da shaye-shaye a wurin.

Hukumar ta ce wannan aikin wani bangare ne na yunƙurin gwamnati a fagen yaƙi da matsalar shaye-shaye da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a ko’ina a faɗin jihar.

Shugaban Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano, Alhaji Tukur Bala Sagagi ya jaddada cewa akwai dokar hana shan shisha a Jihar Kano, don haka gwamnati ba za ta lamunci karya wannan doka ba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *