Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ




Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewar ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, ya miƙa wuya ba gaskiya ba ne.

Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin bayani kan ayyukan sojoji.

Ya ce: “Turji bai miƙa wuya ba. Har yanzu muna neman sa.”

Turji na daga cikin manyan ’yan bindigar da ake nema ruwa a jallo a Najeriya.

Turji ya jagoranci kai wa al’umma hare-hare a Jihohin Zamfara da Sakkwato, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu.

A kwanakin baya, an samu rahotanni cewa Turji, ya ajiye makamai kuma ya saki mut 32 da ya sace, bayan zaman sulhu da malaman addinin Musulunci suka jagoranta a Jihar Zamfara.

Amma sojojin sun bayyana cewa wannan rahotanni ba gaskiya ba ne.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *