Ranar Matasa: Ciyaman ya jinjina wa gwamnatin Gombe kan ɗaukar matasa aiki




Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin GOSTEC aiki a matsayin cikakkun ma’aikata.

Ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnati wajen taimaka wa matasa domin rage zaman banza da kuma ba su damar dogaro da kai.

Ya ƙara da cewa, yanzu wasu daga cikin matasan sun za su hidimata wa al’umma, saɓanin halin da suke ciki a baya.

Ya roƙi matasan su zama masu gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa, inda ya bayyana cewa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma.

Ɗaya daga cikin matasan da aka ɗauka aikin, Musa Abdullahi, ya ce shirin GOSTEC, ya sauya rayuwarsa daga neman aiki zuwa taimakawa wajen bunkasa tattalin arziƙin jihar.

Ita ma, Fatima Mohammed, ta bayyana farin cikinta da samun aikin gwamnati bayan samun horo a fannin shafukan Intanet, tare da yaba wa gwamnati saboda ƙoƙarin inganta rayuwar matasa.

Bikin, ya samu halartar jami’an gwamnati, ƙungiyoyin matasa, inda aka tattauna kan makomar matasa, ilimi da ci gaban tattalin arziƙi a jihar.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *