An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a ya aikata ta’asar.

Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami’an ’yan sanda daga ofishin Zambuk suka hanzarta zuwa wurin, sannan suka mika yarinyar zuwa Asibitin Zambuk domin duba lafiyarta.

Nan take dai rundunar ta cika hannu da wanda ake zargin, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *