Ruftawar ƙasa ta kashe masu haƙar ma’adinai 4 a Filato
[ad_1]
Mutum huɗu sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar da ramin da suke hakar ma’adanan ya yi, a Unguwar Dura da ke Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Mai taimaka wa gwamnan Filato Caleb Mutfwang kan harkokin ma’adanai, Solomon Dung ya bayyana cewa, “Daga abin da aka gaya min, wasu matasa maza suna aiki a cikin wani ramin haƙar ma’adinai, kwatsam ƙasa ta ruguje kan huɗu daga cikinsu.
“Uku suka mutu nan take, kuma an kai wani mutum guda asibiti, kuma abin takaici shi ma daga baya ya mutu.”
A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis ɗin nan da ta gabata.
Wani mazaunin Unguwar, Chuwang Davou ya shaida wa manema labarai a Jos cewa, “Eh, muna da cikin wani mummunan yanayi a Unguwar Dura, wani wurin haƙar ma’adinai ya ruguje a daren ranar Alhamis.
“Ban san adadin waɗanda suka mutu ba, amma ina tabbatar muku da cewa akwai wasu mutane a cikin ramin, lokacin da lamarin ya faru.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link