An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe
Rundunar ’yan sanda ta Jihar Gombe ta samu nasarori a yaƙi da masu aikata laifuka, inda ta kama wata mata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce jami’an sashen kwantar da tarzoma na Anti-Violence Squad sun kama matar mai suna Rakiya Ahmed mai shekaru 53 a unguwar Barunde, inda aka same ta da ƙunshi takwas na ganyen wiwi.
A cewarsa, an cafke matar ce bayan samun sahihan bayanan sirri daga jama’a, kuma yanzu haka ana ci gaba da bincike a kanta.
DSP Abdullahi ya kuma ce rundunar ta cafke wani mutum da ake zargin barawon Adaidaita Sahu ne, da kuma wasu matasa hudu da ake zargin ’yan fashi da makami ne.
Ya bayyana cewa, jami’an ofishin ’yan sanda na Gona sun damƙe mutumin mai suna Auwal Suleiman, mai shekaru 36, a unguwar Nassarawa tare da babur din Adaidaita Sahu da aka sace daga unguwar Wuro Biriji da ke By-pass.
Ya ƙara da cewa, wasu matasa hudu masu shekaru tsakanin 18 zuwa 22 sun shiga wani gida a Hayin Kwarin Misau da makamai, inda suka ƙwace wa mai gidan abinci, kudi da waya, kafin daga bisani rundunar ‘yan sanda ta cafke su.
DSP Buhari ya ce matasan sun amsa laifin da ake zarginsu da shi, kuma an gano wasu daga cikin kayan da suka sace.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Gombe, CP Bello Yahaya, ya yaba wa jami’ansa bisa jajircewarsu, tare da tabbatar da ƙudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyi a jihar.
Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimaka wa jami’an tsaro wajen daƙile miyagun laifuka.