MURIC ta nemi a sauya ranar naɗin Sarkin Ibadan

[ad_1]



Ƙungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta buƙaci kwamitin shirya bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan da ya soke ranar Juma’a, 26 ga Satumba, da aka shirya gudanar da bikin.

Ƙungiyar ta ce wannan rana za ta iya hana ɗaruruwan Musulmi gudanar da Sallar Juma’a da suke yi a kowane mako.

Shugaban MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da aka aika wa manema labarai a ranar Asabar.

Farfesa Akintola ya ce sau biyu irin wannan matsala ta taɓa faruwa a baya: lokacin da aka yi bikin miƙa sandar sarauta ga marigayi Olubadan Oba Akinloye Owolabi Olakulehin da kuma lokacin da aka kaddamar da sabuwar hanyar Iseyin zuwa Ibadan — duka a ranar Juma’a, inda aka samu tangarɗa har Musulmi suka kasa gudanar da Sallar Juma’a.

Ya zargi Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo kan abin da ya kira yunƙurin mayar da ranar Juma’a a matsayin rana ta bukukuwan Kiristoci. Ya ce MURIC ba za ta amince da irin wannan take haƙƙin Musulmi ba.

Saboda haka, ya buƙaci kwamitin shirye-shiryen bikin da ya mayar da ranar Juma’a 26 ga Satumba a matsayin ranar addu’o’in Musulmi domin girmama sabon Olubadan, Oba Rashid Adewolu Ladoja, ko kuma a ɗage bikin zuwa Asabar 27 ga Satumba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *