Mai taɓin hankali ta haihu a tsakiyar kasuwa a Oyo

[ad_1]



Wata mata mai tabin hankali da ba a iya gano danginta ba, ta haihu a bainar jama’a a cikin kasuwar garin Aarinoye a karamar hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa matar ta haihu ne da misalin karfe 5:00;na yammacin ranar Laraba, kuma ta haifi jaririnta namiji lami lafiya ba tare da tallafin unguwar-zoma ba.

Majiyar ta ce kafin matar ta haihu an saba ganinta daga safiya zuwa daren kowace rana dauke da juna biyu tana yawon tsintar dagwalon abinci da shan gurɓataccen ruwa a cikin bola.

idan dare ya yi kuma, majiyar ta ce matar takan koma bayan ginin gidan rediyo na BCOS na Oke Ogun, inda take kwana a kasa ba tare da shimfida ko mayafi ba.

Jim kaɗan bayan haihuwar, mazauna yankin sun hanzarta daukar matakin karbar jaririn daga hannun wannan mata sannan suka mika shi ga babban Jami’in ‘yan sanda (DPO) na yankin.

A nan take ne jami’in ya nemi wasu mata da suka taimaka wajen tsaftace jikin mai jegon da jaririn nata kamar yadda ake yi wa mata masu jego, sannan aka garzaya da ita zuwa wani asibiti a garin Otu hedkwatar karamar hukumar Itesiwaju domin kula da lafiyarta.

Rundunar ’Yan sanda a Jihar ta Oyo ta nemi al’ummar wannan yanki na Aarinoye da su taimaka da ingantaccen bayanin da zai kai ga gano dangi ko mijin wannan matar mai tabin hankali.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *