Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr

[ad_1]

A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League.

Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi.

Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara.

Kafin haka, ya shafe shekaru bakwai yana murza leda a Real Sociedad bayan fitowa daga makarantar horas da kwallon kafarta, sannan ya shafe shekaru shida a Bilbao.

Martinez, wanda ya buga wa kasar Spain wasanni 21 tsakanin 2013 zuwa 2023, ya koma Al-Nassr wadda ta kare a mataki na uku a gasar Saudi Pro League a kakar da ta gabata, wadda Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa mafi zura kwallaye da kwallaye 25.

Tasha

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *