John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi

[ad_1]



Shahararren ɗan wasan wrestling, John Cena, ya samu nasarar lashe kambun Intercontinental a karon farko a tarihinsa.

Cena ya lashe kambun ne da yammacin jiya Litinin, bayan ya doke Dominic Mysterio a birnin Boston, ƙasar Amurka.

Da wannan nasarar, yanzu John Cena ya cika burinsa na lashe dukkan manyan kambuna da ake bugawa a gasar wrestling.

Ɗan wasan mai shekaru 48, wanda ake sa ran zai yi ritaya a watan Disamba mai kamawa, ya zuwa yanzu ya lashe kambuna 17 a gasannin daban-daban da ya shiga.

Tuni dai Cena ya bayyana cewa bayan ritayarsa zai mayar da hankali wajen fitowa a fina-finan Hollywood, kuma ana tsammanin zai gwabza wasansa na ƙarshe a ranar 13 ga watan Disamba, 2025.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *