Esta: Wahalhalun da ake fuskanta a Najeriya ba za su dawwama ba — Shettima
[ad_1]
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa wahalhalun da ake fuskanta a yanzu ba za su dawwama ba.
Ya ce al’amura za su inganta ƙarƙashin manufofin Shugaba Bola Tinubu.
“Ina da tabbaci cewa idan muka haɗa kai, muka yi sadaukarwa, kuma muka yi imani da ƙasarmu, za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen,” in ji shi.
Shettima, ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Abuja, ta bakin mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, a sakon bikin Esta.
Ya ce gwamnati na aiki tuƙuru domin samar da zaman lafiya, farfaɗo da tattalin arziƙi, da kuma gina ci gaba mai ɗorewa.
Ya ƙara da cewa gyaran ƙasa na buƙatar haƙuri, sadaukarwa da haɗin kai daga jama’a.
Mataimakin shugaban ƙasar, ya ce yana da ƙwarin gwiwa cewa Najeriya za ta shawo kan matsalolin tattalin arziƙi da na tsaro da ake fuskanta a yanzu.
Ya ƙara da cewa duk da wahalhalun da mutane ke ciki, ƙasar ba ta taɓa kasa cimma manufofinta ba.
Shettima ya buƙaci ’yan Najeriya su ci gaba da zama a haɗe tare da goyon bayan gyare-gyaren da gwamnati ke yi.
Ya ce ci gaba na buƙatar haƙuri da juriya, tare da haɗin kai.
Haka kuma, ya roƙi jama’a su guji rabuwar kawuna, su rungumi abubuwan da ke haɗa su a matsayin al’umma ɗaya.
Ya ce bambancin da ke tsakanin ’yan Najeriya yana daga cikin manyan ƙarfinsu.
Da yake magana kan muhimmancin Esta, Shettima, ya ce wannan lokaci yana tunatar da Kiristoci muhimmancin sadaukarwa da kuma sabuwar rayuwa.
Ya bayyana cewa Esta alama ce ta nasara kan baƙin ciki da kuma haske a kan duhu.
“Esta tana tunatar da mu cewa waɗanda ba su yanke ƙauna ba za su yi nasara. Tana nuna yadda fata na gari ke tasiri a kan wahala,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link