Sin Ta Fitar Da Takarda Kan Ka’idojin Gudanar Da Harkokin Fasahar AI A Fannin Al’adun Zamantakewar Al’umma
[ad_1]
Ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta Sin da sauran hukumomi guda tara sun fitar da takarda mai taken “Matakan duba ayyukan amfani da fasahar AI a fannin al’adun zamantakewar al’umma,” inda aka ba da shawarar tallafa wa kirkire-kirkiren fasahohi wajen duba ayyukan amfani da fasahar AI a fannin al’adun zamantakewar al’umma, da kuma karfafa amfani da hanyoyin fasaha don hana haifar da abubuwa masu hatsari ga al’adu yayin gudanar da harkoki da amfani da fasahar AI.
Takardar ta bukaci a mai da hankali kan samar da alherin abin ga dan’adam, da tabbatar da adalci, da kuma ikon sarrafawa da amincewa yayin duba ayyukan fasahohin AI a fannin al’adu. Wannan ya hada da duba ko ka’idojin zabar bayanai na horo sun dace, ko an dauki matakai don hana nuna wariya, da kuma ko an bayyana yiwuwar afkuwar abubuwa masu hatsari yadda ya kamata da sauransu.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link