CBN Ya Ɗage Tsarin Dijital, Zai Biya Mahajjata Kuɗin Guzurinsu A Hannu
[ad_1]
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince a biya kuɗin alhazai da tsabar kuɗi a Hajjin 2026. Matakin ya biyo bayan roƙon NAHCON ƙarƙashin shugabancin Ismail Abba Yusuf.
A wata wasiƙa daga sashin kula da kuɗi, bankin ya ce amincewar ta shafi shekarar 2026 kaɗai. Ya kuma jaddada cewa daga 2027 za a koma tsarin biyan kuɗi na katin dijital gaba ɗaya.
- CBN Ta Amince Wa Bankin Masana’antu Buɗe Sashin Bankin Da Babu Riba
- Ƴan Nijeriya Sun Cire Tiriliyan ₦36.3 Ta ATM Cikin Watanni 6 Duk Da Ƙarin Kuɗin Caji — CBN
Matakin ya samu karɓuwa daga masu ruwa da tsaki musamman alhazai masu shirin tafiya. An bayyana damuwa kan ƙarancin ilimin fasaha da matsalolin amfani da katin a Saudiyya.
Masana sun ce wannan ba janye manufar kuɗi zamani ba ne, illa gyara akan lokaci. Sun jaddada cewa tsarin dijital zai inganta tsaro da gaskiya a harkar kuɗi.
NAHCON ta fara shirin wayar da kan alhazai kan sabon tsarin kafin 2027. Ana sa ran haɗin gwiwa da bankuna da gwaje-gwaje zai taimaka wajen sauyin.
[ad_2]
Source link