2027: Obi Da Kwankwaso Za Su Fafata Da Atiku Wajen Neman Takarar Shugaban Kasa A ADC
[ad_1]
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi murabus a hukumance a jam’iyyarsa ta NNPP, inda ya sanar da sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Shigowar Kwankwaso cikin ADC ta tayar da tattaunawa kan hadin gwiwarsa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, don samun tikitin shugaban kasa na jam’iyyar a 2027.
- Sin Ta Fitar Da Mizanin Kasa Na Kyautata Nagartar Na’urar Adana Lantarki
- Ba Za A Iya Daidaita Batun Mashigin Hormuz Ba Har Sai An Kawo Karshen Yaki
An samu labarin cewa tafiyar Obi zuwa Kano kwanan nan a lokacin watan Ramadan ta bude hanyar tattaunawar tsakanin manyan ‘yan siyasar guda biyu.
Sannan kuma an bayyana cewa Obi ya yi alkawari yin wa’adi daya kawai idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa domin samun kuri’un ‘yan arewaci, yayin da arewa za ta nemi dawowa kann mulki a 2031.
Majiyoyi sun ce sauya shekar Kwankwaro zuwa ADC na nuna babban sauyi a siyasa yayin da dan takarar daga arewa maso yamma zai iya haduwa da dan takara daga kudu maso gabas don kayar da shugaban kasa daga jam’iyyar APC.
Haka kuma wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa manyan shugabannin ADC na neman yanayi, inda Obi da Kwankwaso za su yi hadin kai a takarar shugaban kasa, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar zai iya goyon bayan tikitin.
“Wani abu ne da muke aiki a kai, kuma akwai kwarin gwiwa mai karfi na cewa tsohon gwamnan Jihar Kano yana da dubban magoya baya a arewa maso yamma wadanda za su kara yawan kuri’un Obi idan ya samu damar tsayawa takara a zaben fitar da gwani na kai tsaye,” in ji wata majiya.
Sai dai kuma sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya musanta wannan hadaka game da tikitin Obi da Kwankwaso, yana mai cewa kawai, ‘A’a. Ba gaskiya ba ne.’
Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, Abdullahi ya karyata ra’ayin cewa ADC ta bai wa Kwankwaso matsayin abokin takarar Obi. “A’a. Ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
Kazalika, majiyoyi sun shaida cewa jam’iyyar na da sha’awar samu yarjejeiya ta hanyar tara manyan ‘yan takarar shugaban kasa don su shiga cikin shirye-shiryenta.
An sanar da sauya shekar Kwankwaso ta hanyar wata sanarwa da aka fitar ranar 29 ga Maris, 2026, wacce ya sanar da yin murabus daga NNPP, yana bayyana bukatar sake tsara dabaru don amsa canje-canjen siyasa a kasar.
Ya ce, “Ina so in sanar da a hukumance game da yi muraus dina daga jam’iyyar NNPP nan take,” in ji shi, ya kara da cewa wannan shawara, duk da wahalar ta, ta zama dole domin ba shi damar shiga wani jam’iyyar siyasa wanda ke ba da mafi kyawun damar sauya kasa.
Kwankwaso, wanda ya yi aiki a matsayin jagorar jam’iyyar NNPP kuma dan takarar shugaban kasa a 2023, ya yi godiya ga shugabancin jam’iyyar, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Ajuji Ahmed da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da kwamitin amintattu na kasa da mambobi jam’iyyar a dukkan matakai bisa goyon bayansu a lokacin da yake cikin jam’iyyar.
Har ila yau, ya amince da kugiyarsa ta Kwankwasiyya a matsayin wata kungiyar siyasa mai karfi a matakin tushe wanda aka yarda cewa ta kara tasirin NNPP, musamman a Jihar Kano da wasu sassan arewacin Nijeriya.
“Za mu ci gaba da hada kai da yin aiki tare don tsara makoma mafi kyau da kyawun yanayi ga kasarmu ta gado,” in ji shi.
Murabus din Kwankwaso ta zo ne kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC, wanda aka tsara a ranar Litinin da misalin karfe 12 na rana a Jihar Kano.
A wani martani ga lamarin, NNPP ta tabbatar da cewa ta san da shirin barin jam’iyyar da Kwankwaso ya yi kuma tana bibiyar yanayin sosai.
Sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya ce sanarwar farko ta fito ne daga kungiyar Kwankwasiyya amma ya lura cewa jam’iyyar ta dauki sanarwa ta hukuma game da wannan lamari.
“Mun san da shirin barin jam’iyya, kuma a makonni masu zuwa, ana sa ran wasu ‘yan jam’iyya za su kuma bi shi zuwa sabon jam’iyyar siyasa da ya tafi,” in ji Johnson.
Mai magana da yawun NNPP ya amince cewa ficewar Kwankwaso na iya haifar da karin masu sauya sheka, ya nuna damuwa game da rage karfin jam’iyyar, musamman a yankunan arewacin da tafi karfi.
Ana sa ran cewa kungiyar Kwankwasiyya za ta yi aiki tare da Obidients, kungiyar da ke goyon bayan Mista Peter Obi don samun tikitin shugaban kasa a ADC.
Ficewar Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da manyan ‘yan siyasa a fadin kasar da jam’iyyun siyasa ke sake tsara matsayinsu kafin zaben da ke tafe.
Ana ganin shigar Kwankwaso jam’iyyar ADC zai kara habaka matsayin jam’iyyar bisa la’akari da kwarewar siyasarsa da kuma karfin goyon baya a arewa maso yamma.
[ad_2]
Source link