’Yan bindiga sun sace mutum 10 a sabon hari a Kaduna

[ad_1]



Rahonni daga jihar Kaduna na nuni da cewa wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutum; ciki har da mutum bakwai ’yan gida ɗaya da maƙwabtansu guda uku.

Lamarin ya faru ne a unguwar Sabon-Titi da ke kan hanyar Katari zuwa Hayin Dam, a cikin Ƙaramar Hukumar Kachia.

Wani mazaunin yankin mai suna Markus Yakubu, ya bayyana wa manema labarai cewa maharan sun far wa unguwar ne da misalin ƙarfe 9:32 na daren ranar Alhamis.

A cewarsa, maharan sun kutsa cikin gida na farko, inda suka yi awon gaba da mutum bakwai, kafin daga bisani su kwashe wasu mutum uku daga maƙwabtansu.

“’Yan bindigar sun zo da yawa inda suka kewaye gidan maƙociyata. Ba su yi harbi ba a lokacin da suke cikin gidan saboda kusancinsa da gidan DPO ɗin ’yan sandan Katari.

“Sai bayan da suka fito da mutanen waje ne sannan suka fara harbin mai kan uwa da wabi,” in ji Yakubu.

Waɗanda aka sace sun haɗa da: Jummai Amos, Barnabas Amos, Iko Amos, Baby Amos, Eunice Amos, Eshiwan Amos, da Godwin Amos. Ragowar ukun kuma su ne: Bagudu Damisa, Evelyn Damisa, da Alfred Iriyo.

Wani shugaban al’umma a yankin, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da ya yi na tuntuɓar jami’an tsaro a daidai lokacin da harin ke faruwa, abin ya faskara.

A halin yanzu, jami’an tsaro sun bazama cikin dazuka da ke maƙwabtaka da yankin domin gano maɓoyar maharan da nufin ceto waɗanda aka sace.

Sai dai kuma, har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka tura masa ba dangane da lamarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *