Sin Ta Bukaci Amurka Da Isra’ila Da Iran Su Dakatar Da Yaki Nan Take


Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, amfani da karfin soja ba zai iya magance matsala ba. Sin tana sake yin kira ga bangarorin yakin Amurka da Isra’ila da Iran da su dakatar da ayyukan soji nan take, da kuma warware matsalar ta hanyar tattaunawa, ta yadda za a guje wa kawo mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya da wadatar makamashin duniya.

Mao Ning ta bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum da aka gudanar yau Alhamis yayin da take amsa tambaya game da sanarwar shugaban Amurka Donald Trump cewa Amurka za ta ci gaba da kai hare-hare masu tsanani kan Iran. Ban da haka kuma, yayin da take amsa tambayar da ta shafi batun dangantakar Afghanistan da Pakistan, Mao Ning ta ce, bangaren Sin ya dade da goyon bayan bangarorin biyu su warware sabaninsu ta hanyar tattaunawa, kuma zai ci gaba da ba da muhimmiyar gudummawa wajen saukaka halin da ake ciki da kuma kyautata huldar kasashen biyu.

Dangane da karuwar matsayin Sin a cikin jerin kasashe masu kirkire-kirkire kuwa, Mao Ning ta ce Sin za ta inganta karfinta a fannin kimiyya da fasaha, da kuma bunkasa ci gaban duniya baki daya ta hanyar amfani da fasaha.(Safiyah Ma)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *