Shin Bunkasar Sabbin Fasahohi Na Iya Illata Walwalar Jama’a?


A halin yanzu, tattalin arzikin kasar Sin na kara bunkasa bisa tafarkin ci gaba mai inganci, duk kuwa da yadda ake fuskantar tarin kalubale masu sarkakiya a matakai daban daban. A daidai wannan gaba, wasu kafafen watsa labarai na kasashen yamma, suna aza alamar tambaya dangane da tasirin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ga ci gaban zaman rayuwar al’ummar kasar.

A wannan gaba da sabbin fannonin fasaha, irinsu kirkirarriyar basira ko AI, da fasahohin dijital, da na sarrafa hajoji ta amfani da mutum-mutumin inji, da bangarorin harhada laturoni na “semiconductors” ke kara bunkasa a Sin, wasu kafofin yammacin duniya na cewa irin wannan ci gaba na Sin, na tattare da wasu matsaloli, ciki kuwa har da batun tattare albarkatu a fannin manyan fasahohi, da tauye sashen tattalin arzikin jama’a, wanda hakan a cewarsu, na iya haifar da koma bayan daukacin sassan tattalin arzikin kasar baki daya.

To sai dai kuma Bahaushe kan ce “Mai daki shi ya san inda yake masa yoyo”. Domin kuwa har kullum, manufofin bunkasa kasa na Sin na tabbatar da mayar da bukatun jama’a gaban komai. Suna kuma kokarin samar da daidaito tsakanin bunkasar tattalin arziki da kuma cimma walwalar jama’a.

Ana iya ganin hakan karara, a dukkanin sassan rayuwar al’ummun kasar. Wato a duk sassan kasar Sin, jama’a suna more muhimman muradu na samun tsaro da walwala. Yayin da a daya bangaren, kasar ke ta kokarin bunkasa fannonin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, domin cimma nasarar dogaro da kai.

Bangaren masana’antu, ba wani fage ne dake shanye albarkatu kadai ba, maimakon hakan, fanni ne dake samar da riba mai yalwa, wanda tasirinsa ke yaukaka kudaden shiga na al’umma, da samar da karin guraben ayyukan yi, da dogaro da karfin kai a fannin kere-kere.

Daga wannan, za mu iya gano cewa har kullum, kasar Sin na daidaita kokarinta na gina kasa da kuma inganta moriyar al’umma. Wato dai duk wani jarin da Sin ke zubawa a yau wajen bunkasa fannonin fasaha, gini ne wanda daukacin al’ummun kasar za su ci moriyar a gobe, sabanin kuskuren fahimta na wasu daga kafafen yammacin duniya.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *