Jakadan Sin a Najeriya Ya Gana Da Shugaban Kwamitin Kula Da Makarantun Noma Da Cibiyoyin Bincike Na Majalisar Dattawa Ta Najeriya
[ad_1]
Jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai, ya gana da shugaban kwamitin kula da makarantun noma da cibiyoyin bincike na majalisar dattawa ta Najeriya Sharafadeen Ali, jiya Laraba.
Jakada Yu ya bayyana cewa, dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Najeriya ta ci gaba da hawan sabbin matakai tun bayan kulla ta shekaru 55 da suka gabata, musamman bayan ziyarar shugaban Najeriya Bola Tinubu a shekara ta 2024, an samu sakamako mai yawa daga hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban. Ya ce a bana ita ce shekarar farko ta aiwatar da shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15, kuma Sin za ta kara fadada bude kasuwarta ga ketare, kuma nan ba da dadewa ba za ta aiwatar da tsarin shigo da kayayyakin kasashe 53 na Afirka da suka kulla alaka da ita ba tare da karbar haraji ba, wanda zai taimakawa bangaren Najeriya wajen ci gaba da aiwatar da shirinta na “sabunta buri”. Bugu da kari, ya ce ofishin jakadancin yana fatan karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da majalisar dattawan Najeriya, don kiyayewa da kuma ciyar da dangantakar kasashen biyu gaba.
A nasa bangare, Sharafadeen Ali ya godewa bangaren Sin saboda goyon bayan da ya dade yana bayarwa ga ci gaban noma a Najeriya, kuma yana mai fatan karfafa hadin gwiwa da Sin, don inganta fasahar noma da tabbatar da wadatar abinci, da kuma ba da kyakkyawar hidima ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasar. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link