Binciken CGTN: Kusan Kashi 90% Na Masu Amsa Tambayoyi Sun Ce Yaduwar Makaman Nukiliya Da Hatsarin Rashin Kiyaye Su Na Karuwa

[ad_1]

Hare-haren soji da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran na ci gaba da karuwa, inda wuraren nukiliya da dama, ciki har da tashar wutar lantarki ta nukiliya ta Bushehr ta Iran, ke zama wuraren da ake ta hankoron kai wa hari daya-bayan-daya. Sannan, barazanar afkawa yakin nukiliya a kan al’ummomin duniya na kara bayyana a fili. Wani bincike da CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya ya nuna cewa, kashi 89.2 cikin 100 na masu amsa tambayoyi suna ganin cewa, yaduwar makaman nukiliya da hatsarin rashin kiyaye suna karuwa cikin hanzari.

Kasar Sin ta gabatar da shawarar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a fannin kiyaye hatsarin nukiliya, inda ta jaddada cewa, karfafa tsarin kiyaye hatsarin nukiliya na kasa da kasa ba wai kawai muhimmin sharadi ne ga bunkasar masana’antar makamashin nukiliya ba, har ma wani muhimmin bangare ne na inganta tsarin kula da tsaron duniya, da bullo da sabon salo na dangantakar kasa da kasa, da kuma kyautata tsarin zaman duniya. A cikin binciken na jin ra’ayoyi, kashi 84.2 cikin 100 na masu amsa tambayoyi sun nuna cikakken goyon baya ga wannan shawara ta Sin, inda suka yi amannar cewa, sai an samar da yanayin kasa da kasa mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne kadai za a iya magance matsalolin ta’addancin nukiliya da yaduwar makaman nukiliya gaba daya.

An gudanar da kuri’ar jin ra’ayoyin ce a dandalolin CGTN na harsunan Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci da Rashanci, inda masu amfani da intanet 12,768 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *