Daga “yaro mai gyaran babur” zuwa zakaran duniya: Labarin nasarar Zhang Xue mai dogaro da karfin samar da kayayyaki na kasar Sin

[ad_1]

A ranar 28 ga watan Maris na 2026, lokacin da kamfanin Zhang Xue na kera babura ya lashe gasar WSBK ta Portugal a kan manyan kamfanoni a wannan fanni a duniya kamar Ducati da Yamaha, mai kamfanin Zhang Xue ya zubar da hawayen farin ciki. Zhang Xue ya kwashe shekaru 20 yana dukufa kan sana’arsa ta kera babura, tun lokacin da yake matashin mai gyaran babura wanda ya kammala karatun sakandare kawai. Ya tsahi daga dan kauyen tsaunuka na Hunan zuwa zakara a duniya. Labarinsa, wani misali ne na yadda tsarin zamanintar da al’ummar Sinawa ke samar da yanayi mai kyau ga jama’ar kasar.

Shekaru sama da goma da suka gabata, Zhang Xue, mai gyaran babura, ya tafi birnin Chongqing da kudi Yuan dubu 20 kawai don cimma “burinsa na kera babura”, saboda Chongqing shi ne “babban birnin babura na kasar Sin,” inda a kasuwar kayayyakin babura daya kawai, za a iya samun dukkan kayayyakin harhada babur.

Chongqing ya samu wannan fifiko ne saboda kokarin da aka yi a cikin goman shekarun da suka gabata. A shekarun 1970, kasar Sin ta fara kera baburan Jialing 50 da kanta a birnin Chongqing. A shekarun 1990 kuma, yawan baburan da aka samar a Chongqing ya kai fiye da kashi 60% na yawan baburan da aka kera tare da sayar da su a kasar Sin. A shekara ta 2019, aka fara sanya masana’antar kera babura a matsayin babbar masana’anta ta birnin Chongqing. Ya zuwa shekara ta 2025, yawan baburan da aka kera a birnin Chongqing ya kai miliyan 7.857, wanda ya zama na farko a manyan biranen kasar Sin; yawan baburan da birnin ya fitarwa kasashen waje ya kai miliyan 6.109, wanda ya kai fiye da kashi 1/3 na dukkan adadin kasar Sin; kana akwai manyan kamfanonin kera babura 51 da kamfanonin kera kayayyakin babura 410 a birnin. Cikakken tsarin masana’antu da aka tara cikin shekaru 40 da suka wuce, ya marawa Zhang Xue baya, kuma wannan “fa’idar tsarin” tana haifar da karin “Zhang Xue” a birnin Chongqing.

Zhang Xue ya sha cewa, “Muddin akwai zanen da ya shafi tsarin babur, ana iya kera kowane bangare na babur a kasar Sin, kuma ingancinsa ba zai yi kasa da na Turai, Japan da Amurka ba.” Zhang yana da kwarin gwiwa mai inganci bisa cikakkun nau’ikan masana’antu da Sin take da su, wato daga inji zuwa tsarin lantarki, daga kwarangwal din babur zuwa taya, duk ana iya kera su a kasar Sin.

A lokaci guda, yanayin masana’antun kasar Sin ya canza daga “mai bin bayan sauran kasashe” zuwa “tafiya tare da sauran kasashe” da kuma “jagora a duniya” a wasu fannoni. Babur din Zhang Xue mai samfurin 820RR yana dauke da tsarin lantarki na IMU mai nau’in axis 6, kuma daga injin zuwa tsarin lantarki, duk kamfaninsa ne ya kirkiro tare da kera su da kansa. A shekara ta 2025, darajar kayayyakin da kamfanin ya kera ya kai Yuan miliyan 750, kuma kudaden da aka kashe don gudanar da bincike sun kai Yuan miliyan 69.58. A shekara ta 2026, kudin bincike da aka kebe zai kai Yuan miliyan 135. Matakan da suka bayyana yadda masana’antun samar da kayayyaki na Sin su ke karkata zuwa yanayi mai matukar inganci bisa kokarin mai da hankali kan inganta fasaha.

Ci gaban mutum tana tafiya daidai da ci gaban kasa. Labarin Zhang Xue ya tabbatar da cewa a kasar Sin, kowa zai iya cika burinsa muddin yana da mafarki da kwarin gwiwa da kwarewa da hazaka. Wannan shi ne fa’idar tsarin zamanintar da al’ummar Sinawa—wato cikakken tsarin masana’antu, kasuwa mai bude kofa, da girmama kwarewa, wadanda suka hada kai wajen marawa mutane baya a kokarinsu na neman samun nasara.(Mai zane da rubutu: MINA)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *