Abin Da Ya Kamata A Sani Game Da Gasar Cin Kofin Duniya Ta Bana
[ad_1]
Jiya Talata aka kammala buga wasannin share fagen shiga Gasar kofin Duniya na FIFA da za a fara a watan Yunin wannan shekarar a kasashen Amurka, Mexico da Canada, kasashe 6 ne suka samu damar shiga gasar a Daren Jiya ciki har da kasar Congo wadda ta fitar ta Nijeriya a matakin wasannin share fage bayan ta doke kasar Jamaica da ci 1 mai ban haushi.
Wannan ne karo na farko da kasashe 48 zasu buga gasar cin kofin Duniya, hakazalika gasar ya bana ita ce karo na 23 da za a buga kofin mai dimbin tarihi, an shafe fiye da shekara 1 ana buga wasannin share fagen shiga Gasar a nahiyoyi 6 dake fadin Duniya, inda aka fara tun a watan Satumbar shekarar 2023.
Kasar Bosnia-Herzegovina ta fitar da kasar Italiya wadda ta lashe kofin sau hudu a tarihi yayinda Jamhuriyar Czech, Turkiyya da Sweden suma suka samu damar zuwa gasar a ranar karshe,
Wasanni 104 za a buga a tsakanin kasashe uku da zasu karbi bakuncin gasar inda za a gudanar a birane 16, daga cikin biranen 11 ne a kasar Amurka, uku a Mexico sai biyu a Kanada, za a kuma shafe tsawon kwanaki 39 ana fafatawa sabanin kwanaki 29 da aka shafe wajen buga gasar a kasar Qatar a shekarar 2022, kasar Mexico ce za ta kara da Afirka ta Kudu a filin wasa na Estadio Azteca dake Mexico City a wasan farko na gasar kwanaki 18 bayan kammala kakar gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Kasar Spain na daga cikin kasashen da ake hasashen cewa zasu iya lashe gasar ta bana bayan sun samu nasara a gasar cin kofin kasashen Turai, duba da cewar tanada manyan yan wasa irinsu Pedri, Fabian Ruiz, Rodri wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024 da Lamine Yamal, wanda yana daya daga cikin mafi kyawun yan wasa matasa a Duniya.
Kasashe 4 ne zasu buga gasar a karon farko a tarihinsu, daga cikinsu akwai kasar Curacao wadda zata zama kasa mafi kankanta da za ta buga gasar cin kofin Duniya idan ta fafata da kasashen Jamus, Ivory Coast da Ecuador a rukunin E, Curacao, mai nisan mil 37 daga gabar tekun Venezuela, tana da yawan jama’a 150,000 kwatankwacin wata karamar hukuma a Nijeriya.
[ad_2]
Source link