Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Ziyarci Kasar Seychelles

[ad_1]

Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Seychelles tsakanin 28 zuwa 30 ga watan nan na Maris, bisa gayyatar da takwaransa na Seychelles Sebastien Pillay ya yi masa.

A birnin Victoria, fadar mulkin kasar ta Seychelles, Han Zheng ya tattauna da shugaban kasar ta Seychelles Patrick Herminie, kana ya gana da Sebastien Pillay. Kazalika, ya halarci liyafar bikin cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Seychelles.

Yayin tattaunawarsa da shugaba Herminie, Han Zheng ya ce alakar Sin da Seychelles na gudana bisa salo na kawance, da daidaito, da tallafawa juna, da cimma moriyar juna tsakanin babbar kasa da kananan kasashe. Ya ce yayin dandalin FOCAC na tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, an daga matsayin alakar kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.

Han Zheng ya kara da cewa, Sin ta yi matukar jinjinawa bangaren Seychelles, bisa cikakken goyon bayansa ga batutuwan dake shafar manyan moriyar kasar Sin. Ya ce a baya-bayan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da janye dukkanin harajin kwastam kan kayayyakin da kasashen Afirka 53 masu alakar diflomasiyya tare da Sin ke shigarwa Sin, tun daga ranar 1 ga watan Mayun bana.

Han Zheng ya kara da cewa, kamata ya yi Sin da Seychelles su ci gaba da aiki tare don tabbatar da Seychelles ta mori manufar janye harajin. Ya ce har kullum Sin za ta ci gaba da nacewa salon cudanyar mabambantan sassa, kana a shirye take ta yi aiki tare da Seychelles, wajen kare adalci a matakin kasa da kasa, da kare doka da moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa.

A nasa bangare kuwa, mista Herminie cewa ya yi, a halin yanzu, alakar Seychelles da Sin ta kai matsayin koli a tarihinta. Kuma bangaren Seychelles na nacewa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, ta kuma yi matukar jinjinawa shawarwarin bunkasa ci gaban duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar. Bugu da kari, bangaren Seychelles a shirye yake, ya zurfafa hadin gwiwa a sassa daban daban tare da Sin, da kuma ingiza babban ci gaba a alakar Seychelles da Sin. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *