Taɓarɓarewar Sabis: NCC Ta Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Biya Diyya
[ad_1]
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta umurci kamfanonin sadarwar wayar hannu (MNOs) da su biya diyya ga masu amfani da layukan waya waɗanda ke fuskantar matsalar ƙarancin ingancin sabis na sadarwa a wasu wurare.
Hukumar ta bayar da wannan umarni ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi ta bakin Nnenna Ukoha, shugabar sashen hulɗa da jama’a, inda ta jaddada cewa bai kamata a ce, duk matsalolin sabis za su riƙa ƙarewa ne akan masu amfani da sabis ba, idan kamfanonin sadarwa sun gaza cika ƙa’idojin da aka gindaya na bayar da ingantaccen sabis ba.
A cewar sanarwar, “A ƙarƙashin wannan umarni, kamfanonin da suka saɓa ƙa’ida za su biya masu amfani da sabis din, wadanda tabarbarewar sabis ya shafa kai tsaye saboda karya ma’aunin ingancin sabis (QoS).
“Za a tilasta wa kamfanonin sadarwar wayar hannu (MNOs) su biya wannan diyya a duk lokacin da aka samu ƙarancin ingancin sabis a cikin wa’adin da aka kayyade.
“Za a bayar da diyya ne ta hanyar ƙarin kuɗin kira (airtime), wanda za a lissafa daidai da yawan wadanda lamarin ya shafa, da kuma yankin da karancin sabis din ya faru.”
[ad_2]
Source link