Kasar Sin Ta Hau Matsayi Na 9 A Ma’aunin Kirkire-Kirkire A Duniya
[ad_1]
Yau Lahadi, cibiyar nazarin tsare-tsaren ci gaba na kimiyya da fasaha ta Sin ta fitar da rahoton ma’aunin kirkire-kirkire na kasa na Sin na shekarar 2025 a gun taron shekara-shekara na dandalin Zhongguancun.
Rahoton ya gina tsarin nuna ma’aunin ne bisa fannoni biyar: albarkatun kirkire-kirkire, kirkirar ilimi, kirkirar kamfanoni, ingancin kirkire-kirkire, da kuma shugabancin kirkire-kirkire, don kimanta karfin kirkire-kirkire na kasashe 60 a duk duniya. Sakamakon ya nuna cewa Sin tana matsayi na 9 a duniya a cikin ma’aunin kirkire-kirkire na kasa, kuma tana ci gaba da tafiya zuwa cimma burinta na zama kasa mai karfin gaske a fannin kimiyya da fasaha.
Idan an kwatanta da shekarar 2012, matsayin kasar Sin ya haura sama da matsayi 11, wanda hakan ya sanya ta zama kasa mafi saurin bunkasa a cikin shekaru goma da suka gabata, kuma kasa daya tilo da ke da matsakaicin kudin shiga da ta shiga cikin manyan kasashe goma a duniya.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link