Bayelsa United Ta Lallasa Kano Pillars 4-1 A Yenagoa


Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sha kashi mai nauyi bayan Bayelsa United ta doke ta da ci 4-1. Wasan ya gudana a filin Samson Siasia da ke Yenagoa a mako na 32 na NPFL.

Kano Pillars ta shiga wasan da burin samun nasara domin inganta matsayinta a teburin gasar. Sai dai ƙoƙarinta bai yi nasara ba bayan ta kasa tsayawa kan harin abokan karawarta.

  • Kano Pillars Ta Doke Enyimba, Ta Matsa Gaba A Teburin Gasar NPFL
  • Kano Pillars Ta Ƙare Zagayen Farko Na Gasar Firimiyar Nijeriya A Jan Layi

Bayelsa United ta zura dukkan ƙwallayenta huɗu ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci. Wannan ya jefa Pillars cikin matsin lamba mai tsanani har zuwa ƙarshen wasa.

Pillars ta samu ƙwallo ɗaya ta hannun Williams Ayuba a ƙarshe. Amma hakan bai hana Bayelsa United tabbatar da cikakkiyar nasara a wasan ba.

Sakamakon ya sa Kano Pillars ta koma matsayi na 16 da maki 39 a wasanni 32. Hakan ya ƙara jefa ta cikin matsin lamba a fafatawar kakar bana.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *