Yakin Amurka/Israila Da Iran: Bukatar Takin Urea Ya Yi Matukar Karuwa


Yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin Kasar Iran da Kasashen Isara’ila da Amurka, ya yi sanadiyyar karuwar bukatar Takin Zamani, musamman na Urea.

Yakin dai, ya shafi kasuwannin duniya wajen samar da Takin na Urea, musamman duba da cewa; yakin ya sanya wasu kasashen duniya, na ta faman kai komo na son samun Takin Urea, domin shirin fara noman bana.

Kazalika, yakin ya kuma yi sanadiyar rufe babbar mashigar Hormuz tare da kuma rufe masana’antun da ake sarrafa Takin Zamani a yankin Gulfda da kuma sauran wasu manyan hanyoyin da ake yin amfani da su wajen safarar Takin na Urea.

Babbar mashigar ta Hormuz, ba wai kawai ana yin amfani da ita wajen safarar danyen mai ba ne, har da ma hada-hadar safarar Takin Zamani a duniya.

A cewar wani ma’aikaci a masana’antar sarrafa Takin Zamani ta Indorama, “Tun bayan da aka fara yakin, muna ci gaba da ganin karin bukatar ta Takin na Urea,”.

Ma’aikacin ya kara da cewa, amma muna mayar yin duba ne a kan abokan cinikinmu, kafin mu amshi bukatarsu ta Takin Zamani.

Ana sa ran wannan bukatar ta Takin na Urea, zai kara bunkasa kudaden shiga na Takin da aka fitar daga cikin kasar zuwa ketare, musamman ganin cewa; akwai dimbin irin wannan Taki a kasar.

A kasar nan dai, akwai masana’antu guda uku da suka yi fice, wadanda suka hada da Notore, Indorama da kuma ta Dangote, wadanda daukacinsu ke sarrafa Takin Zamanin da yawansa ya kai kimanin tan miliyan 6.5.

Misali, a shekarar 2023, wadannan masana’antu sun samar da kimanin tan miliyan 3.65 na Takin na Urea.

Kasancewar Gas shi ne jigo da ake yin amfani da shi wajen sarrafa sinadaran ammonia da na nitrogen da ake hada Takin na Urea, tun bayan fara yakin farashin sa a Tarayyar Turai, ya karu da kashi 50 cikin dari.

Hakan ya tilastawa manyan masu sarrafa Takin na Urea a Gabas ta Tsakiya, suka rage yawan adadin Takin na Urea da suke sarrafawa.

A cewar kafar yada labarai ta Bloomberg, sakamakon wannan tsadar farashi na Gas a kasuwar duniya, hatta babbar masana’antar sarrafa Takin Zamani da ke Kasar Slobakiya, ita ma ta sanar da rage yawan adadin Takin Zamanin da take samarwa.

A cewar tsohon sakataren kungiyar masu sarrafawa da kuma rabar da Takin Zamani na kasa, Gideon Negedu, an samu raguwar bukatar sinadarin hada Takin Zamani na ammonia da nitrogen da kuma na Urea, wadanda kuma dukkaninsu kasar nan na samar da su.

Ya bayyana cewa, a yanzu ana ci gaba da nuna bukatar Takin na Urea, da masana’antun cikin kasar ke samarwa, wanda kuma dole ne a kara zagewa, wajen kara mayar da hankali wajen sarrafa shi, domin a cike gurbin bukatar da ake da ita ta Takin na Urea.

Kazalika, kafar yada labarai ta Bloomberg, ta ruwaito mataimakin shugaban rukunonin kamfnin Dangote, Debakumar Edwin, ya sanar da cewa; kamfanin na ci gaba da samun karin bukatar ta Takin na Urea, musamman daga kasuwar duniya

“Bukatar ta Takin na Urea, ta karu daga kasuwar duniya saboda karancinsa da ake da shi a kasuwar duniya,” in ji Edwin.

Bugu da kari, ana sa ran wannan bukatar da ake da ita ta Takin na Urea a kasuwar duniya, za ta kara habaka hada-hadar fitar da kaya daga cikin kasar nan zuwa kasashen ketare.

A cewar wasu alkaluma da sashen hada-hadar kasuwanci a majalisar dinkin duniya ya fitar, a shekarar 2024 kacal, Nijeriya ta samu ribar kimanin dala miliyan 850 daga Takin Urea da fitar zuwa ketare.

Haka zalika, wannan alkaluma sun kuma nuna cewa; duk a shekarar ta 2024, Nijeriya ta fitar tan miliyan 3.2 na Takin na Urea zuwa kasuwar duniya.

Farashin Buhun Takin na Urea mai nauyin kilo 50 a cikin kasar nan 11 ya karu da kashi 11 a cikin dari, wato daga naira 33,000 zuwa Naira 36,500 kan farashin da aka sayar a makon da ya gabata.

Hakan na kuma kara jefa fargaba a zukatan al’ummar da ke fadin kasar nan, wadda ake yi wa lakabi da mafi yawan al’umma na nahiyar Afirka.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *