Gobarar Tashar Jabi: Da rigar jikina kawai na tsira
[ad_1]
’Yan kasuwa na ƙoƙarin gano girman asarar da suka tafka bayan gobarar da ta tashi mako guda bayan Ƙaramar Sallah ta Tashar Motoci ta Jabi da ke Abuja.
Wani matashin dan kasuwar da ya tsallake rijiya da baya a gobarar ya bayyana cewa “Da rigar nan ta jikina na tsira,” bayan tashin wutar a yayin da yake kwance a cikin shagonsa a Kasuwar.
Wani wanda ya ce bai san abin da ya faru ba a kasuwar sai da aka kaita shi a waya ya ce, “da na ɗaga waya sai aka ce min ya wannan hali da muke ciki? Ne ce wan hali kuma, me ya faru? Aka ce min an duk shagunanmu sun ƙone. Yanzu komai ya zama toka. Sai dai addu’ar Allah Ya mayar da alheri.”
Aminiya ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3.30 dare ta yi ta ci har zuwa bayan karfe bakwai na safe, ko da yake ba a kai ga gano musabbinta ba.
Wani mai sana’ar cutar kuɗi na POS, ya ce, ”Komai nawa ya ƙone, sai injin POS ɗaya kawai da na tsira da shi.”
“Cash da nake da su sun jone a cikin shafin, komai ya zama toka, babu abin moruwa a cikin kayan,” in ji wani matashin cikin damuwa.
Wani dattijo a kasuwar da bai bayyana sunansa ba ya ce, “Allah Ya taimaka ’yan kwana-kwanan sun zo da wuri, ba don haka ba da munin abin yafi haka.”
“Manyan wayoyi da duk kayan da ke cikin shagon wani mai waya duk duk sun kone.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link