Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe
[ad_1]
Ƙaramar Hukumar Gombe, ta raba wa mata masu juna guda 400 kayan haihuwa kyauta, domin kare lafiyarsu da rage mace-mace a yankin.
An gudanar da rabon ne a Cibiyar Haihuwa ta Gombe a ranar Alhamis, inda shugaban Ƙaramar Hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya jagoranci rabon.
Shugaban ya ce shirin ya yi daidai da umarnin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na bunƙasa kiwon lafiya a matakin farko, musamman ga mata masu juna biyu daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa haihuwa.
Ya kuma bayyana cewa an fara gwajin jini kyauta ga mata masu juna biyu a dukkanin cibiyoyin haihuwa, domin gano matsalolin lafiya tun da wuri.
Wasu daga cikin matan da suka amfana sun gode wa gwamnati, inda suka bayyana cewa shirin zai rage musu kashe kuɗi tare da tabbatar da lafiyarsu da ta jariransu.
Wata mata mai suna Sa’adatu Garba, ta bayyana jin daɗinta game rabon kayan.
“Wannan kaya da aka ba mu tabbas za su taimaka, musamman duba da halin matsi da ake ciki,” in ji ta.
Ita kuwa Rabi Mustapha cewa ta yi: “Wannan babban tagomashi ne, muna godiya Allah Ya saka da alheri. Wannan shiri zai sauƙaƙa mana wajen rage kashe kuɗaɗe.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link