Shawarar Gina Alummar BilAdama Mai Makomar Bai Daya Ta Sin Na Ci Gaba Da Share Fagagen Ci Gaban Duniya

[ad_1]

Shekaru 13 tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya fara gabatar da shawarar nan ta gina alummar biladama mai makomar bai daya ga kowa, cikin jawabinsa a jamiar Moscow State Institute of International Relations dake kasar Rasha, shawarar ta ci gaba da zama wani ginshiki mai karfi na saita alkiblar bunkasa da ci gaban duniya.

Cikin wadannan shekaru 13, shawarar ta bunkasa daga wani tunani zuwa muhimmin ginshikin aiwatar da manufofi na hakika. Har ma alummun sassan duniya daban daban, na ta kara fahimtar tasirinta, da karfinta na zama tushen ci gaba a fayyace. Wannan shawara ta zama wata fitila mai haske dake haskaka wa biladama tafarkin samun ci gaba daga mabanbantan fannoni.

A wannan duniya ta yau, mai fama da tarin sauye-sauye da rashin tabbas, rungumar manufar cimma moriyar juna ta daukacin biladama a dogon lokaci, na da tarin alfanu sama da duk wasu lokuta da suka gabata a baya. Biladama na kara fuskantar tarin kalubale, irinsu salon murdiya, da siyasar nuna karfin tuwo, da daukar matakan kashin kai, da kariyar cinikayya, yayin da a daya bangaren, tsarin cudanya tsakanin mabambantan sassa, da cinikayya cikin yanci ke fuskantar turjiya. Hakan ya sa masharhanta da dama ke ganin wannan shawara ta kasar Sin, ta dace da halin da ake ciki. Duba da cewa ta tanaji salo na cimma moriya tare, da hadin gwiwa na gudu tare a tsira tare.

Burin shawarar gina alummar biladama mai makomar bai daya ga kowa, ya dace da sharuddan samar da ci gaban zamantakewar danadam, kana ya yi daidai da kudurorin wanzar da zaman lafiya da ci gaban dukkanin sassa. Kazalika, tana aikewa da sako na hakika, cewa a yayin da ake tunkarar kalubale na bai daya, ba wata kasa ko yanki da zai cimma nasara shi kadai. Wato dai hadin gwiwa, da aiki kafada da kafada, su ne kadai hanyoyin cimma nasara ga kowa.

Kamar dai yadda shugabannin kasar Sin suka sha nanatawa, ta hanyar aiki tukuru, Sin za ta yi tafiya tare da dukkanin sassa, wajen wanzar da wannan manufa ta gina alummar biladama mai makomar bai daya ga kowa, daga shawara zuwa sakamako na hakika, ta yadda za ta kai ga haifar da gudummawa ga ci gaban duniya, da bunkasar rayuwar daukacin biladama. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *