Wang Yi Ya Yi Kira Da A Dauki Matakan Dakile Kara Tabarbarewar Yanayi A Gabas Ta Tsakiya


Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce daya daga abubuwan dake sahun gaba a yanzu, shi ne dakatar da yaduwar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, da dakile shigar karin kasashe cikinsa.

Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi tsokacin ne a jiya Jumma’a, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarci ga shugaban kasar Faransa kan harkokin siyasa Emmanuel Bonne, bisa gayyatar da mista Bonne din ya yi masa.

Ya ce amfani da karfin tuwo ba zai warware matsalar da ake ciki ba, kana bai dace a kyale yakin rashin adalci ya ci gaba da wakana ba. Wang Yi ya kara da cewa, a yayin da ake fuskantar yanayi mai tsanani, ya dace Sin da Faransa a matsayinsu na membobin dindindin a kwamitin tsaron MDD, su karfafa tuntubar juna, da tsara matakai bisa matsayin koli, kana su goyi bayan kundin tsarin mulkin MDD da dokokin kasa da kasa, kuma su kare duniya daga tsunduma cikin yanayi na danniya da fin karfi.

A nasa bangare kuwa, Bonne bayyana mahangarsa ya yi dangane da halin da ake ciki yanzu haka a Gabas ta Tsakiya, ciki har da abubuwan dake wakana a Iran da Lebanon. Ya ce Faransa a shirye take ta inganta tuntuba da hadin gwiwa tare da Sin, domin ingiza matakin cimma zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Saminu Alhassan)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *