Tsaro: DSS Ta Ceto Sakataren Ƙaramar Hukuma A Kano


Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da ceto Sakataren Gudanarwa na Ƙaramar Hukumar Kibiya, Alhaji Hamza Durya, kwanaki bayan da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace shi.

An sace Durya ne a daren Juma’a a gidansa da ke ƙauyen Durya, a Ƙaramar Hukumar Kibiya, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki yankin suka tafi da shi.

  • Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Dakatar Da Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano
  • Yunƙurin Hana Gawuna Bin Kwankwasiyya, “An Neme Shi A Waya An Rasa”

Majiyoyin tsaro sun bayyana tun da fari cewa maharan, kimanin su shida, sun iso ne a kan babura kuma suka aiwatar da harin cikin gaggawa ba tare da harbi ko guda ba.

Shaidun gani da ido sun ce, ‘yan uwan sakataren suna tare da shi a lokacin da maharan suka zo, amma ba su cutar da kowa ba, kawai dai, sun zo sace sakataren ne.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Waiya, ya fitar a ranar Laraba, gwamnatin ta ce jami’an Hukumar Tsaro ta DSS ne suka gudanar da samamen na haɗin gwiwa wanda ya kai ga ceto wanda aka sace tare da kama mutum biyu da ake zargi.

Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun samu raunukan harbin bindiga a yayin aikin ceton.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *