Kasar Sin Ta Bayar Da Kyautar Sabon Rukunin Kayayyakin Kiwon Lafiya Ga Madagascar
[ad_1]
An gudanar da bikin mika kyautar kayayyakin kiwon lafiya da kasar Sin ta bai wa Madagascar, a birnin Antananarivo, babban birnin kasar ta Madagascar a jiya Talata 24 ga wata.
An ce, bisa ga tsarin hadin gwiwar asibitocin Sin da kasashen Afirka, a wannan karo, asibiti na farko na jami’ar Lanzhou ta kasar Sin ne ya samar da kayayyakin ga asibitin Anosiala na kasar ta Madagascar, ciki har da na’urorin da ake amfani da su wajen jinyar masu cututtukan numfashi.
Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta kasar Madagascar ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin kasar Sin da ma kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasar da ke aiki a Madagascar bisa gudummawar da suka samar.
Jakadan kasar Sin a Madagascar Mr. Ji Ping ya ce, kyautar kyayyakin kiwon lafiya da aka mika a wannan karo, ta kara inganta hadin gwiwar kasashen biyu ta fannin kiwon lafiya, wadda kuma ta shaida niyyar kasashen ta karfafa hadin gwiwarsu. (Lubabatu Lei)
[ad_2]
Source link