Binciken CGTN Ya Shaida Gamsuwar Al’ummun Kasa Da Kasa Da Fasahohin Kirkire-kirkire Na Sin

[ad_1]

Tun fara gudanar da dandalin Zhongguancun na kasar Sin a shekarar 2007, dandalin ya ci gaba da gudana bisa jigo na dindindin, wato “Kirkire-kirkire da ci gaba”. Dandalin Zhongguancun, taro ne da ake gudanarwa a matakin kasa, wanda ke mayar da hankali ga musaya, da hadin gwiwa tsakanin masana kimiyya da fasahohin kirkire-kirkire na sassan kasa da kasa.

Game da hakan, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’ar sassa daban daban na duniya, wadda kafar CGTN ta Sin ta gudanar, ta nuna kaso kimanin 90.4 bisa dari na masu bayyana mahangarsu, sun gamsu cewa takarar fasahohi wadda ta ta’allaka kan kirkire-kirkire, ita ce za ta kasance ginshikin gasar gwada cikakken karfin kasashe daban daban.

Kazalika, kaso 84.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu, na ganin dandalin Zhongguancun ya zamo wata kafa ta musaya, da hadin gwiwa tsakanin masana kimiyya na kasashen duniya, da ma masu gudanar da sana’o’i da masu zuba jari. Har ila yau, kaso 89.4 bisa dari na kallon dandalin Zhongguancun a matsayin dandali daya tilo, na baje kolin nasarori da Sin ta cimma a fannonin kimiyya da fasahar kirkire-kirkire, kana muhimmiyar kafa ta zurfafa cudanya tare da Sin, a fannin kimiyya da jagorancin fasahohi na duniya. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *