Kwankwaso na tattaunawa da jam’iyyun ADC da NDC

[ad_1]



Ƙungiyar Kwankwasiyya ta tabbatar da cewa jagoran NNPP kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, na ci gaba da tattaunawa da jam’iyyun ADC da kuma NDC gabanin zaɓen 2027.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Mansur Kurugu, ya shaida cewa tattaunawar na gudana ne da yiwuwar haɗa ƙarfi tsakanin ɓangarorin siyasar, duk da cewa har yanzu ba a cimma matsaya kan wace jam’iyya za a su koma ba.

A cewarsa, “Gaskiya ne Kwankwaso na tattaunawa da ADC da NDC, kuma muna da yaƙinin cewa a ƙarshe za a zaɓi wata jam’iyya guda kafin Zaɓen 2027.”

Ya ƙara da cewa wasu manyan ‘yan siyasa da suka haɗa da Peter Obi da Seyi Makinde da kuma Seriake Dickson na daga cikin waɗanda ake tattaunawar, wadda ya ce ta yi nisa sosai.

Taron masu ruwa da tsaki da Kwankwaso ya yi tare da Peter Obi a Kano

Kurugu ya bayyana cewa a ƙarshe shugabannin za su iya zaɓar ɗaya daga cikin jam’iyyun ADC ko NDC, ko kuma su ci gaba da amfani da New NNPP a matsayin inuwar siyasa da za su zauna a ƙarƙashinta.

A ranar Lahadi ne wasu manyan jiga-jigan hamayyar siyasar Najeriya suka kai wa Kwankwaso ziyara a gidansa da ke Kano, inda daga bisani aka gudanar da taro na siyasa da ɗaruruwan magoya baya suka halarta.

Cikin waɗanda suka kai ziyarar sun haɗa da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar LP, Peter Obi da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson da sauransu.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya ce ’yan siyasar sun kai masa ziyarar gaisuwar sallah ne.

Dukkannin ’yan siyasar dai na cikin jam’iyyu mabanbanta juna, inda Kwankwaso ke jam’iyyar NNPP, shi kuma Peter Obi ke ADC sai kuma Seyi Makinde da Seriake Dickson da ke PDP.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *