2027: Cikin Ƴan APC Ya Ɗuri Ruwa Saboda Tasirin Makinde  – Ƙungiyar PDP

[ad_1]

Ƙungiyar ƙwararru a PDP ta zargi APC da tsoron Gwamna Seyi Makinde. Ta ce hakan na faruwa ne gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A wata sanarwa, Kodinetan ƙungiyar, Barrista Obinna Nwachukwu, ya bayyana wannan tunan nasu. Ya ce APC na zarge zarge marasa tushe domin karkatar da hankalin gwamnan.

  • 2027: Makinde, Kwankwaso, Dickson Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
  • Gwamna Makinde Ya Gwangwaje Ƴan Wasan Nijeriya da Naira Miliyan 22

Ya jaddada cewa kalaman APC sun nuna tsoron tasirin Makinde a faɗin ƙasa. Ya ce hakan na nuna damuwar jam’iyyar kan karɓuwarsa a idon jama’a.

Ƙungiyar ta kuma zargi APC da matsa lamba kan gwamnoni su sauya sheƙa. Ta ce an yi yunƙurin yaɗa jita-jita kan sauya sheƙar Gwamna Bala Mohammed.

Ta ce jita-jitar ta rushe bayan gwamnan Bauchi ya ƙaryata batun. Ta ƙara da cewa irin waɗannan dabaru na nufin raunana jam’iyyun adawa.

Ƙungiyar ta buƙaci APC ta mayar da hankali kan matsalolin tsaro da tattalin arziki. Ta ce halin da jama’a ke ciki na ƙara tsananta a ƙasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *