Sarauta babu ilimi ba ta da amfani — Sanusi II
[ad_1]
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa girmamawa da hidimar da ta ke yi wa masarautar.
Ya kuma jaddada muhimmancin ilimi ga shugabanci da ci gaban mutum.
Sanusi, ya bayyana hakan ne yayin Hawan Nassarawa da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Kano a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Sallah Ƙarama.
“Muna godiya da girmamawa da karramawar da Gwamnatin Jihar Kano ke yi mana,” in ji Sarkin.
Ya kuma yi bayani kan yadda wasu suka yi magana game da komawarsa makaranta, inda ya ce ba ya koma ba ne game da shari’ar masarautar.
“Komawata makaranta ba saboda batun kotu ba ne, sai dai don ƙarfafa wa wasu gwiwa,” in ji shi.
Sanusi, ya ce ilimi ya fi sarauta muhimmanci.
A cewarsa, ilimi yana taimaka wa shugabanni su yi aiki da kyau kuma su samu girmamawa a cikin al’umma.
“Waɗanda ke sukar komawata makaranta su fahimci cewa ilimi ya fi sarauta muhimmanci,” a cewarsa.
Ya kuma ƙara bayyana muhimmancin ilimi a tsarin sarauta.
“Sarki mai ilimi yana samun ƙarin daraja, amma Sarkin da ba shi da ilimi, sarautarsa ba ta da amfani,” in ji shi.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattaunawa kan shugabanci, al’ada da kuma ilimin zamani a tsarin masarautu.
Hawan Nassarawa, wanda yake daga cikin manyan abubuwan bikin Sallah a Kano, an gudanar da shi a wannan shekara cikin wani salo na daban.
Wannan ya biyo bayan umarnin gwamnatin jihar domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link